Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-kwamandan dake jagorantar yanto yankunan da 'yan ta'adda suka mamaye yace, kama yanzu mun kewaye garin Takrit ta bangarori hudu, Janar Abdulwahab ya kara da cewa, mun yaudari 'yan ta'adda ta inda muka fara kai masu hare-hare ta sama a inda sukayi dan-dazo sannan muka tura sojojin mu ta kasa da nufin 'yanto Takrit amma nufin mu shine 'yanto sauran yankunan Salahuddin.
Kwamandan ya yabi cigaban da sojin kasar ke samu tare da hadin gwiwar sojin sa kai wajan yakar 'yan ta'adda na Da'ish.ABNA